Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Babban kotun tarayya dake Kaduna ta bada belin Nasir El-Rufai

Babban kotun tarayya dake Kaduna ta bada belin Nasir El-Rufai Babban kotun tarayya dake Kaduna ta bada belin Nasir El-Rufai
Babban kotun tarayya dake Kaduna ta bada belin Nasir El-Rufai

Kotun Tarayya da ke Jihar Kaduna ta bayar da beli ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kamar yadda ɗansa, Bello El-Rufai, ya tabbatar.

Bello El-Rufai ya ce iyalansu na cikin kotu kuma suna kokarin ganin an cika dukkan sharuddan belin da kotun ta gindaya, yana mai nuna jin daɗinsu da wannan mataki na shari’a.

Ya bayyana cewa suna mutunta doka da oda, kuma za su tabbatar an bi dukkan umarnin kotu domin kammala tsarin belin cikin kankanin lokaci.

Lauyan wanda ake tuhuma, Ubong Akpan (SAN), ya ki yin cikakken bayani ga manema labarai.

Haka kuma, wani jigo a jam’iyyar ADC, Hayatudeen Lawal Makarfi, ya tabbatar da bayar da belin tare da cewa an gindaya wasu sharudda da ake sa ran za a cika cikin gaggawa.

Tun da farko, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu, inda aka dage sauraron bukatar belin zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use