Rundunar ƴan sanda ta jihar Abia ta fara farautar wani ɗan sa-kai da ake zargi da kashe budurwarsa tare da raunata wasu mutane biyu a yankin Amakama da ke Umuahia ta Kudu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Umuanga Amakama, inda ake zargin wanda ake nema ya kai hari kan budurwarsa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta nan take, yayin da wasu biyu suka jikkata.
An kai waɗanda suka jikkata asibiti domin ba su kulawa, yayin da aka ajiye gawar mamaciyar a dakin ajiya domin bincike.
Rundunar ‘yan sanda ta ce tana ci gaba da bincike tare da neman wanda ake zargin, sannan ta yi kira ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannu domin tabbatar da zaman lafiya.