Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Iran ta buɗe mashigar Hormuz ga jiragen kasuwanci
ADC ta yi kira ga Tinubu da ya shirya fuskantar fushin ƴan Najeriya a 2027
An fille kan matashi a Filato

ADC ta yi kira ga Tinubu da ya shirya fuskantar fushin ƴan Najeriya a 2027

ADC ta yi kira ga Tinubu da ya shirya fuskantar fushin ƴan Najeriya a 2027

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kamata ya ji tsoron shan kaye a zaben 2027, tana mai cewa zai fuskanci miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fama da matsanancin hali a ƙarƙashin gwamnatinsa.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta soki kalaman shugaban ƙasar inda ta ce ba su dace da matsayinsa ba, tana mai zargin sa da mai da hankali kan siyasa maimakon magance matsalolin talauci da rashin tsaro.

Jam’iyyar ta ce a daidai lokacin da ‘yan ƙasa ke fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashin abinci da kuma ƙaruwar basussuka, shugaban ƙasa ya fi mayar da hankali wajen sukar ‘yan adawa maimakon ɗaukar matakan rage wahalhalu.

Haka kuma ADC ta ƙaryata zargin cewa ta gudanar da taronta a kan titi, tana mai cewa an hana ta amfani da wuraren taro na gwamnati, abin da ta ce na nuna yadda sararin dimokuraɗiyya ke ƙara takaituwa a ƙasar.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa matsalolin da ke addabar ƙasar sun haɗa da rashin tsaro, talauci, tare da jaddada kudirinta na gina madadin shugabanci mai inganci da zai kawo sauyi ga ‘yan Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use