’Yan bindiga sun kashe wani matashi mai shekara 30, mai suna Elisha Abbas Saku, ta hanyar fille masa kai a Ƙaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis a kauyen Riwhie-Chwo da ke Nzharuvo, yankin Miango, inda mazauna suka ce maharan sun shiga yankin ne da misalin ƙarfe 10 na dare.
Ƙungiyar Matasan Irigwe ta tabbatar da aukuwar kisan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, inda ta bayyana harin a matsayin mummunan ta’addanci da ya girgiza al’umma.
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar, Joseph Yonkpa, ya ce maharan sun yi wa mamacin kwanton bauna kafin su fille masa kai, yana mai addu’ar Allah ya bai wa iyalansa da al’ummar Irigwe haƙurin jure wannan rashi.
Babu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sandar jihar ta Filato har izuwa lokacin rubuta wannan rahoton.