Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka ta bankaɗo shirin China na bai wa Iran makaman kariya – Rahoto

Amurka ta bankaɗo shirin China na bai wa Iran makaman kariya - Rahoto Amurka ta bankaɗo shirin China na bai wa Iran makaman kariya - Rahoto
Shugaban Amurka, Donald Trump

Rahotanni daga kafafen yada labarai, ciki har da CNN da Reuters, sun nuna cewa hukumar leƙen asiri ta Amurka ta gano alamun cewa China na shirin tura sabbin makaman kariya daga hare-haren sama zuwa ƙasar Iran cikin makonni masu zuwa.

Rahoton ya ce wannan bayanin ya samo asali ne daga mutane uku da ke da masaniya kan rahotannin leƙen asiri na baya-bayan nan.

A cewar rahoton, makaman da ake zargin China na shirin tura wa Iran sun haɗa da na’urorin kariya daga hare-haren jiragen sama da ake iya ɗauka a kafaɗa, waɗanda aka fi sani da MANPADS.

An kuma bayyana cewa China na iya amfani da wasu ƙasashe a matsayin hanya ta ɓoye asalin jigilar makaman domin kauce wa gano kai tsaye.

Rahoton ya kuma ce wannan mataki na iya zama abin tayar da hankali, musamman ganin cewa Beijing ta bayyana cewa ta taimaka wajen sasanta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka da ta dakatar da rikicin da ke gudana na makwanni shida a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai kuma ofishin jakadancin China a Washington ya musanta zargin, inda ya ce China ba ta taɓa bai wa kowane ɓangare makamai a wannan rikici ba, kuma bayanan da ake yadawa ba gaskiya ba ne.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use