Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Mohammed Hayatu-Deen, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, inda ya bayyana cewa halin matsin tattalin arziki da ƙasar ke ciki ne ya tilasta masa ɗaukar wannan mataki.
Hayatu-Deen ya nuna damuwa kan yadda rayuwar al’umma ke ƙara tsananta, yana mai cewa wahalhalun tattalin arziki sun kai matakin da ke buƙatar sabuwar hanya ta siyasa domin ceto ƙasar daga halin da take ciki.
Ya kuma yi zargin cewa dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar koma baya, inda ya ce wasu matakai da ake ɗauka a harkokin siyasa na rage amincewar jama’a ga tsarin mulki da kuma zaɓe.
A cewarsa, shiga jam’iyyar ADC wani yunƙuri ne na haɗa kai da masu ra’ayi iri ɗaya domin samar da ingantacciyar siyasa da kuma kawo sauyi mai ma’ana a ƙasar, musamman gabanin zaɓen 2027.