Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Rundunar sojin Najeriya ta koka kan ƙarancin masu shiga aikin daga yankin Kudu maso gabas
Morocco ta saki magoya bayan Senegal bayan zaman gidan yari kan rikicin AFCON

Morocco ta saki magoya bayan Senegal bayan zaman gidan yari kan rikicin AFCON

Hoto a lokacin da ake rikicin AFCON

Rahotanni sun bayyana cewa an saki wasu magoya bayan ƙasar Senegal da aka tsare a Morocco bayan sun kammala hukuncin zaman gidan yari na watanni uku, inda aka miƙa su ga jami’an ofishin jakadancin Senegal.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutanen uku sun bar gidan yari na Al Arjat 2 da ke Rabat, sannan aka kai su ofishin ’yansanda kafin daga bisani a miƙa su ga jami’an diflomasiyyar Senegal.

Sakin nasu ya biyo bayan kammala hukuncin da ya shafi zargin ta da rikici da hayaniya a lokacin wasan karshe na cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da aka gudanar a birnin Rabat.

Rahotanni kuma sun nuna cewa har yanzu akwai wasu magoya bayan Senegal kusan 15 da ke ci gaba da zaman gidan yari, bayan kotu ta tabbatar da hukuncin su da ya kai daga watanni shida zuwa shekara guda kan zarge-zargen tayar da tarzoma da lalata kayayyaki a lokacin wasan.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use