Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026
Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, inda aka amince da jimillar kashe kuɗi na tiriliyan ₦68.32 domin tafiyar da harkokin gwamnati a shekarar.

Kasafin kuɗin ya haɗa da manyan bangarori kamar kuɗin tafiyar da gwamnati, biyan bashin ƙasa, da kuma ayyukan ci gaba, inda aka ware kaso mai tsoka domin gina ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.

A lokaci guda, shugaban ya kuma amince da wani gyara da ke tsawaita aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 daga ranar 31 ga Maris zuwa 30 ga Yuni, 2026.

Gwamnati ta bayyana cewa wannan tsawaitawa zai bai wa hukumomi damar kammala manyan ayyukan raya ƙasa da ke dab da ƙarewa, musamman waɗanda suka shafi gine-gine da ababen more rayuwa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use