Ɓangaren jam’iyyar PDP da ke samun goyon bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya karɓi ikon sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja daga hannun jami’an ‘yan sanda.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai na ɓangaren Wiken, Muhammad Jungudo ya fitar, ta ce jam’iyyar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ko tashin hankali a sakatariyar ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ’yan sanda sun miƙa ginin ne ga Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdulrahman Mohammed Takushara, da kuma Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, bisa umarnin kotu.
Rikicin kan ikon ginin ya ƙara ƙamari ne tun a watan Nuwamba, lokacin da ɓangaren Wike ya yi arangama da ɓangaren da ke samun goyon bayan gwamnonin Bala Mohammed da Seyi Makinde.