Gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutane da ƙungiyoyi 48 da ake zargi da hannu a ko tallafa wa ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar.
Hukumar da ke kula da sanya takunkumi ta Najeriya ce ta bayyana jerin a ranar Asabar, a wani mataki da ta ce yana cikin ƙoƙarin yaki da tallafin kuɗi ga masu ta da zaune tsaye.
Sunayen da aka fitar sun haɗa da mutane da ƙungiyoyi da bincike ya danganta da ayyukan ta’addanci, ciki har da IPOB, Ansaru, da ISWAP, waɗanda gwamnati ta riga ta haramta.
Daga cikin waɗanda aka ambata a jerin sunayen akwai Simon Ekpa, Tukur Mamu, Yusuf Ghazali, Mercy Ali, Ohagwu Juliana, Abdulsamat Ohida, Mohammed Sani, Fatima Ishaq, Abubakar Muhammad, Kubara Salawu, Eze Okpoto, Nwaobi Chimezie, Rabiu Suleiman, tare da wasu da dama daga sassa daban-daban na ƙasar.
Gwamnati ta ce za ta rufe asusun bankuna da toshe duk wata hanyar kuɗi na waɗanda aka ambata a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin dakile ayyukan ta’addanci a Najeriya.