Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

NAHCON ta gargadi al’umma su guji shiga hannun ‘yan damfara wajen neman bizar aikin Hajji

NAHCON ta gargadi al’umma su guji shiga hannun ‘yan damfara wajen neman bizar aikin Hajji NAHCON ta gargadi al’umma su guji shiga hannun ‘yan damfara wajen neman bizar aikin Hajji
Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta gargadi al’ummar Najeriya, musamman masu niyyar zuwa aikin Hajji, da su guji fada wa hannun ‘yan damfara da ke ikirarin samar da bizar Hajji ta haramtacciyar hanya.

Hukumar ta bayyana cewa wasu bata-gari na ci gaba da yaudarar jama’a ta hanyar karɓar kuɗi suna yi musu alƙawarin samar da takardun izinin zuwa Hajji, wanda abu ne hakan da ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.

A cewar NAHCON, hukumomin ƙasar Saudiyya sun riga sun rufe bayar da bizar Hajji, kuma babu wata dama ta samun izini ta wata hanya daban, sai ta hanyoyin da aka amince da su kawai.

Hukumar ta jaddada cewa duk wanda ya bi ta haramtacciyar hanya zai iya fuskantar hukunci mai tsanani, ciki har da cin tara, kora daga Saudiyya ko kuma hana shi shiga aikin Hajji baki ɗaya.

NAHCON ta buƙaci duk masu niyyar zuwa aikin Hajji da su bi hanyoyin da suka dace ta hannun hukumomin da aka tantance, tare da yin taka-tsantsan domin guje wa shiga tarkon masu zamba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use