Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun yi barazanar dakatar da aiki saboda tsadar mai
Kotu a Afrika ta kudu ta yanke wa Julius Malema hukuncin daurin shekara biyar

Kotu a Afrika ta kudu ta yanke wa Julius Malema hukuncin daurin shekara biyar

Kotun ta yanke wa Julius Malema hukuncin daurin shekara biyar Kotun ta yanke wa Julius Malema hukuncin daurin shekara biyar
Julius Malema

Wata kotu a Afirka ta Kudu ta yanke wa jagoran jam’iyyar adawa, Julius Malema, hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari bisa samunsa da laifin amfani da bindiga ba bisa ƙa’ida ba.

A same shi da laifi ne bayan ya harba bindiga a sama yayin wani gangamin siyasa da ya gudana a shekarar 2018, abin da kotu ta ce ya saba dokokin mallakar makamai.

Malema, wanda shi ne shugaban jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), ya musanta zargin tun farko, yana mai cewa abin da ya aikata wani bangare ne na bikin siyasa.

Sai dai kotu ta jaddada cewa irin wannan aiki na da haɗari ga jama’a, musamman ganin matsalar amfani da bindiga da ke addabar ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa lauyoyinsa na shirin ɗaukaka ƙara, yayin da masana ke ganin hukuncin na iya yin tasiri ga makomar siyasarsa a nan gaba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use