Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa babu wata barazana ko matsin lamba da zai hana shi ci gaba da jagoranci da manufofinsa gabanin zaɓen 2027.
Tinubu ya bayyana kansa a matsayin “Jagaban,” yana mai jaddada cewa ba zai bari adawa ko haɗin gwiwar wasu jam’iyyu su razana shi ko su dakile shirinsa na cigaban ƙasa ba.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin ana samun motsi da haɗin gwiwa tsakanin wasu ‘yan adawa domin tunkarar zaɓen 2027, wanda ake sa ran zai kasance mai zafi a fagen siyasar Najeriya.
Shugaban ya kuma bayyana cewa yana da cikakken ƙuduri na ci gaba da aiwatar da manufofinsa na gyaran tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma, duk da kalubalen da ake fuskanta.