Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta kwashe adadi mai yawa na ‘yan gudun hijira zuwa garin Monguno domin tsira daga hare-haren ‘yan ta’adda da ke ƙara kamari a yankin.
A cikin wata sanarwa da Laftanar Ayodeji Abiodun, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soji a Hedikwatar Sashe na 3 na Operation Hadin Kai da ke Monguno, ya fitar, ya bayyana cewa an samar da sabbin wuraren zama na wucin gadi domin tsugunar da waɗannan ‘yan gudun hijira.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayanan sirri sun nuna cewa wasu daga cikin mazauna sansanonin Gana Ali da Stadium na bai wa ‘yan ta’adda mafaka, musamman a lokutan da suke kai hare-hare kan sansanonin sojoji a yankin.
Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa ‘yan ta’addan na hana sauran mazauna yankin da kuma jami’an sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) shiga wasu daga cikin sansanonin, ciki har da Gana Ali da Stadium da ke Monguno.
Rundunar Sojin ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.