Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Atiku ya zargi Tinubu da gazawa

Atiku ya zargi Tinubu da gazawa Atiku ya zargi Tinubu da gazawa
Atiku ya zargi Tinubu da gazawa

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da nuna gazawa da rashin ƙwarewa a shugabanci.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana kalaman Tinubu na baya-bayan nan a matsayin “maganganu marasa tushe balle makama” waɗanda ke nuna gazawa da rashin iya shugabanci.

Da yake mayar da martani, Atiku ya ce abin mamaki ne yadda shugaban ƙasa da ake ta ce-ce-ku-ce kan sahihancin takardunsa zai yi ƙoƙarin ɓata sunan wasu da ke da tabbataccen tarihin hidimar jama’a.

Game da batun sayar da kadarorin gwamnati, ɓangaren Atiku ya ce sukar da Shugaba Tinubu ya yi ba ta da tushe idan aka yi nazari sosai, inda suka tunatar da cewa a baya shugaban ya taɓa nuna adawa da irin waɗannan gyare-gyare da yanzu yake ƙoƙarin aiwatarwa.

Atiku ya ƙara da cewa irin waɗannan kalamai daga shugabanci na iya jawo rudani a cikin al’umma, tare da kira da a mayar da hankali kan inganta shugabanci da warware matsalolin da ke addabar ƙasa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use