Hukumar kula da magunguna ta Najeriya (PCN) ta rufe gidajen sayar da magani guda 598 a Jihar Kaduna, sakamakon keta dokoki da ka’idojin aikin sayar da magani.
Haka kuma, hukumar ta kama mutane biyu yayin wani gagarumin aikin sa ido da tilasta bin doka da aka gudanar na tsawon kwanaki huɗu a sassa daban-daban na jihar.
Shugaban Sashen Aikace-aikace na hukumar, Suleiman Chiroma, ya bayyana cewa an gudanar da bincike kan wurare 828 a ƙananan hukumomi 10 na jihar domin tabbatar da bin ka’idojin aiki.
A cewarsa, wuraren da aka bincika sun haɗa da kantunan magani 123, shagunan sayar da magungunan patent 631, da kuma wurare 74 marasa lasisi, inda aka gano laifuka daban-daban da suka saba wa ƙa’ida.
Chiroma ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da tsauraran dokoki da kare lafiyar jama’a daga amfani da magungunan da ba su da inganci ko kuma ba bisa ƙa’ida ba.