Dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Najeriya sun dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a garin Kukareta da ke Jihar Yobe, inda aka kashe kimanin ‘yan ta’adda 24 a yayin artabun.
Harin, wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis, ya ɗauki kusan sa’o’i uku, yayin da maharan suka yi yunƙurin mamaye wani sansanin soji a yankin.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa bayan harin da aka kai cikin dare, inda aka fara musayar wuta da maharan da misalin ƙarfe uku na safe.
Uba ya ƙara da cewa dakarun sun kai farmaki tare da mayar da martani mai ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya cikin ruɗani.
Haka kuma, ya ce an samu nasarar ƙwato makamai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47 guda 18, manyan bindigogi guda uku, bindigogin PKT guda biyu, RPG guda uku, da gurneti guda huɗu, da sauran kayan yaƙi.