Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan Najeriya ba su da zaɓi face mara wa Tinubu baya a 2027— Fubara

‘Yan Najeriya ba su da zaɓi face mara wa Tinubu baya a 2027— Fubara ‘Yan Najeriya ba su da zaɓi face mara wa Tinubu baya a 2027— Fubara
‘Yan Najeriya ba su da zaɓi face mara wa Tinubu baya a 2027— Fubara

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce ‘yan Najeriya ba su da wani zaɓi face su haɗa kai su mara wa Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu baya domin ya ci zaɓen 2027 mai zuwa.

Fubara, wanda a ƙarshen shekarar da ta gabata ya koma jam’iyyar APC, ya buƙaci ‘yan ƙasar da su goyi bayan shugaban ƙasar a karo na biyu domin ba shi damar ci gaba da aiwatar da manufofinsa.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Kudancin Najeriya da aka gudanar a Fatakwal a ranar Alhamis, Fubara ya bayyana Tinubu a matsayin “mai sadaukarwa kuma mai kishin ƙasa,” wanda ya kamata a ba shi dama ta biyu.

Ya kuma zayyano nasarori daban-daban da gwamnatin Tinubu ta samu a cikin shekarun baya, yana mai hasashen ƙarin ci gaba a ƙarƙashin shirin Renewed Hope idan aka sake zaɓen shugaban ƙasar a 2027.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use