Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Macron ya fara gangamin neman taimako don sake gyara Lebanon

Macron ya fara gangamin neman taimako don sake gyara Lebanon Macron ya fara gangamin neman taimako don sake gyara Lebanon
Emmanuel Macron, shugaban Faransa

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana aniyarsa ta shirya wani taro na ƙasa da ƙasa domin tallafawa sojojin Lebanon tare da taimakawa wajen sake gina yankin kudancin ƙasar da ya lalace.

Macron ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da takwaransa na Cyprus, Nikos Christodoulides, inda ya ce za a gudanar da taron ne a lokacin da gwamnatin Lebanon ta ga ya dace.

Ya ce taron zai kuma mayar da hankali kan samar da ƙarin tallafin kuɗi daga ƙasashen Turai domin taimakawa ƙasar ta farfaɗo daga matsalolin da take fuskanta.

Bugu da ƙari, Macron da Christodoulides sun nuna goyon bayansu ga ƙulla wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa tsakanin Tarayyar Turai da Lebanon, domin ƙarfafa dangantaka da kuma tallafawa ci gaban ƙasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use