Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Peter Obi na ganawar sirri da gwamna Bala Mohammed a Bauchi

Peter Obi na ganawar sirri da gwamna Bala Mohammed a Bauchi Peter Obi na ganawar sirri da gwamna Bala Mohammed a Bauchi
Peter Obi da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi

Jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya kai ziyara jihar Bauchi domin ganawa da gwamna Bala Mohammed.

Ba a bayyana cikakken dalilin ziyarar tasa ba, yayin da manyan ‘yan siyasar biyu suka shiga ganawar sirri a cikin dakin tarbar shugaban ƙasa da ke fadar gwamnatin jihar Bauchi.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin jihar sun ce ana hasashen ganawar na da nasaba da muhimman al’amuran siyasa da kuma shirye-shiryen tunkarar zaɓuka masu zuwa.

Ana sa ran bayan kammala tattaunawar, za su yi wa ‘yan jarida bayani kan abin da aka tattauna.

Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, ya taɓa bayyana a watan Maris cewa ADC na cikin zabin da yake duba yiwuwar komawa.

Sai dai daga baya, ya kuma karɓi bakuncin shugabannin jam’iyyar APC, ciki har da Nentawe Yilwatda da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a farkon watan Afrilu, abin da ya ƙara tayar da tambayoyi kan matsayinsa na siyasa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use