Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojoji sun ce sun hallaka ‘yan ta’adda 30 a tafkin Chadi

Sojoji sun ce sun hallaka ‘yan ta’adda 30 a tafkin Chadi Sojoji sun ce sun hallaka ‘yan ta’adda 30 a tafkin Chadi
Sojoji sun ce sun hallaka ‘yan ta’adda 30 a tafkin Chadi

Dakarun Operation HADIN KAI sun kashe akalla ‘yan ta’adda 30 tare da lalata jiragen ruwansu a wani samame da suka kai a Tafkin Chadi, kusa da tsibirin Kaniram da Ke jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce an kai harin ne daga daren Talata zuwa safiyar Laraba, bayan rundunar sojin sama ta gano jirage da ‘yan ta’addan ke amfani da su.

An kai hare-hare da suka lalata jiragen tare da tarwatsa hanyoyin samar da kayayyakin su.

Har ila yau, a sake kai wasu hare-hare kan masu tserewa, inda aka kara hallaka da dama.

A cewarsa, wannan aiki ya rage karfin ‘yan ta’addan tare da tilasta musu tserewa cikin dazuka.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use