Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa ya amince ya jagoranci hukumar ne kawai bayan ya samu tabbacin a zuciyarsa cewa Allah zai ba shi ƙarfi da taimako a kan wannan nauyi.
Ya bayyana haka ne an Abuja yayin wani taron godiya da Ƙungiyar Baptist ta Najeriya ta shirya domin bankwana da shugaban ta mai barin gado, Israel Akanji, tare da matarsa Victoria.
Amupitan ya ce da bai samu wannan tabbaci na ruhaniya ba, da ya ƙi karɓar muƙamin.
A cewarsa, kafin ya amince da aikin, ya samu saƙo mai ƙarfafawa daga Allah wanda ya ba shi kwarin gwiwar ɗaukar wannan nauyi, yana mai cewa wannan imani ne ya taimaka masa wajen fuskantar ƙalubalen gudanar da zaɓe a ƙasa mai dimokuraɗiyya mai sarkakiya kamar Najeriya.
Ya ƙara da cewa Allah ne ya ci gaba da tallafa masa tun bayan hawansa kan muƙamin, yana mai jaddada cewa babu wani ƙalubale da ya fi ƙarfin ikon Allah.
Amupitan ya kuma roƙi ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar addu’a, musamman domin samun nasarar zaɓen shekarar 2027, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa za a iya gudanar da zaɓe mafi inganci a tarihin ƙasar.