Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik.
Ana zarginsa da yin kutse a wayar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Masu gabatar da kara sun ce laifin ya saba wa dokar Kare Muhimman Bayanai ta Kasa da kuma dokar Cybercrimes ta 2024, bisa wani bayani da ake zargin ya taba furtawa a wata hira da ya yi a wani gidan talabijin.
Sai dai El-Rufai ya musanta zargin, yayin da lauyan gwamnati ya nemi karin kwanaki domin gabatar da shaidu, tare da bukatar a boye bayanan shaidun.
A nasa bangaren, lauyansa ya bukaci kotu ta duba bukatar belinsa, yana mai cewa yana hannun ICPC, yayin da za a ci gaba da shari’ar nan gaba.