Babbar Kotun Jihar Plateau ta tsare wasu mutane huɗu a hannun Hukumar tsaron farin kaya ta DSS kan zargin da ake musu na hannu a kisan da aka yi a watan Maris 2026 a unguwar Angwa Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.
An dage shari’ar zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da jin bahasi.
An samu tsaiko wajen fara shari’ar ne saboda rashin halartar lauyoyin kare masu laifi a zaman kotun.
Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Alla-wadai da harin, yana mai cewa an yi shi ne da nufin tada rikici a jihar, tare da jaddada cewa dole rayuwa ta ci gaba duk da irin wannan tashin hankali.
Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ziyarci jihar a baya-bayan nan, ya gana da wadanda abin ya shafa, inda ya tabbatar musu cewa za a yi adalci kan lamarin.
Wadanda ake tuhuma sun hada da Isa Umar Ibrahim, Auwalu Abubakar (wanda ake kira Auwalu Dogo), Musa Abubakar Ibrahim (wanda aka fi sani da Yaroro), da wasu, inda ake zargin sun hada kai wajen kai harin.
Gwamnati jihar Plateau ce ta shigar da tuhumar a kotu, tana zargin su da hannu a kisan da ya faru a anguwar Rukuba, da ke Jos ta Arewa.