Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

An mayar da gawar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu gida

An mayar da gawar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu gida An mayar da gawar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu gida
Edgar Lungu, tsohon shugaban Zambia

Gwamnatin Zambiya ta ce an mayar mata da gawar tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu, bayan shafe watanni goma ana taƙaddama kan dawo da ita daga Afirka ta Kudu.

Gwamnatin ta Zambia na so a yi wa Mista Lungu jana’izar bangirma a Lusaka, babban birnin ƙasar. Sai dai, iyalansa sun ƙi amincewa da hakan.

An ɗauki gawar ne daga wani wurin ajiyar gawa a daren Laraba ba tare da sanin iyalansa ba, a cewar rahotanni.

Babban lauyan gwamnatin Zambia ya ce babbar Kotun Pretoria ce ta miƙa gawar mista Lungu ga gwamnati.

Hakan ya zo ne bayan da iyalansa suka yi watsi da batun ɗaukaka ƙarar da suka shigar na buƙatar a soke hukuncin cewa a binne tsohon shugaban ƙasar a Lusaka.

Lungu ya rasu bayan fama da rashin lafiya a watan Yunin bara a wani asibiti a Afrika ta Kudu, yana da shekara 68.

Ya mulki Zambiya daga 2015 zuwa 2021, lokacin da ya sha kaye a hannun Hichilema.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use