Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yi la’akari da dakatar da kamfen na siyasa a wasu jihohi takwas na Arewacin ƙasar sakamakon tsananin matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara.
Wannan kira ya biyo bayan damuwa da ake ciki kan sabbin hare-haren ‘yan ta’adda da ke addabar yankin.
An bayyana wannan batu ne a zaman majalisar, inda Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya jaddada cewa ya zama dole a ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka.
Ya ce ba za a ci gaba da harkokin siyasa ba yayin da tsaro ke cikin mawuyacin hali.
Sanatocin sun nuna cewa hare-haren da ake kai wa sansanonin sojoji da kuma fararen hula na nuna cewa an samu koma baya a nasarorin da aka samu a yaƙi da ‘yan tada ƙayar baya, lamarin da ke barazana ga tsaron ƙasa baki ɗaya.
Haka kuma, majalisar ta nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa daruruwan mata, yara da tsofaffi na ci gaba da zama a hannun ‘yan ta’adda a Jihar Borno, inda aka buƙaci gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen ceto su cikin gaggawa.
A ƙarshe, majalisar ta yi kira ga al’umma da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen shawo kan matsalar tsaro, yayin da ta jaddada cewa dole ne a ɗauki matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa.