Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kaduna ta ci gaba fiye da yadda na same ta

Gwamnan Kaduna - Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce a yanzu, jihar ta fi yadda ya same ta a shekarar 2023 sosai, yana mai cewa an samu ci gaba a fannonin tsaro, ilimi, ababen more rayuwa da kuma tattalin arziki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron bita na manyan jami’an gwamnati da Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ta shirya a wani ɓangare na makon hulɗa da jama’a na Najeriya, wanda aka gudanar a Kaduna ranar Asabar.

Ya ce jihar da ya gada tana da dimbin damammaki amma ta kasance cike da matsalolin tsaro, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma raunin alamomin ci gaban zamantakewa.

Uba Sani ya ce: “Kaduna ba ita ce yadda take a baya ba. A yau ta fi kyau sosai, kuma abin farin ciki shi ne cewa tana ci gaba da samun ci gaba tare da shirin cimma manyan nasarori.”

Ya ce tun bayan hawansa mulki a 2023, gwamnatinsa ta aiwatar da muhimman ayyuka da suka haɗa da gina sabbin ajujuwa 736, horar da fiye da ma’aikatan ilimi 33,000 kan sabbin dabarun koyarwa da fasahar zamani, gina hanyoyi, da kuma mayar da dubban manoma gonakinsu bayan inganta tsaro a wasu yankuna.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use