Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Najeriya za ta tura sojoji 200 Turkiyya domin samun horo na musamman

General Christopher Musa, Chief of the Defense Staff of Nigeria

Ministan tsaro, Christopher Musa ya ce Najeriya za ta tura dakaru na musamman 200 domin samun horo a ƙasar Turkiyya nan take.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a gefen taron Diflomasiyya na Antalya karo na biyar da aka gudanar a Antalya, bayan ganawa da takwaransa na Turkiyya, Yasar Guler.

A cewarsa, Turkiyya ta ware guraben horo 200 ga jami’an soji na musamman na Najeriya, kuma za a tura su nan take, inda ya ce wannan mataki zai kara inganta kwarewar sojojin kasar.

Musa ya kara da cewa kasashen biyu za su ci gaba da gudanar da atisayen hadin gwiwa, inda atisaye na farko zai gudana nan gaba a wannan shekara, tare da fadada hadin kai a fannoni daban-daban na tsaro.

Haka kuma, ya bayyana cewa Najeriya da Turkiyya sun amince da hadin gwiwa wajen kera kayayyakin tsaro da musayar fasahar soja, yana mai cewa dangantakar kasashen biyu ta dade tun 1960, kuma Turkiyya na da kwarewa da Najeriya za ta iya anfani da ita.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use