Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki gargadin da Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta fitar, yana mai cewa yunƙuri ne na tauye ’yancin ’yan jarida da takaita ’yancin faɗin albarkacin baki.
A cikin wata sanarwa, NBC ta sanar da dukkan masu watsa shirye-shirye da masu ruwa da tsaki cewa za ta tsaurara mataki wajen tabbatar da cikakken bin dukkan tanade-tanaden dokokin watsa labarai na Najeriya, musamman waɗanda suka shafi adalci, daidaito, sahihanci, kalaman ƙiyayya, tayar da hankali da kuma girmama hukumomin ƙasa.
Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa daga yanzu, duk mai gabatar da shiri da aka samu da laifin bayyana ra’ayi a matsayin gaskiya, cin zarafi ko tsoratar da baƙo, ko hana ba da damar jin ra’ayoyi daban-daban, za a ɗauki mataki a kansa.
Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku ya ce wannan mataki na NBC na nuna yunƙurin murkushe ’yan jarida ne, musamman a daidai lokacin da kafafen watsa labarai na Najeriya ke samun yabo a duniya saboda ƙwarewa da juriyarsu.
Ya ce hukumar tana yawan fito da irin waɗannan tsauraran matakai duk lokacin da zaɓe ke gabatowa, yana mai cewa hakan na iya rufe bakin masu adawa maimakon inganta aikin jarida na gaskiya.
Atiku ya kuma ce dole ne a fahimci cewa ƙa’idojin aikin jarida ba lokacin zaɓe kawai suke amfani ba, illa dai doka ce ta dindindin da kowa ya kamata ya bi.