Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Birtaniya ta yi watsi da matakin soja kan mashigar Hormuz

Birtaniya ta yi watsi da matakin soja kan mashigar Hormuz Birtaniya ta yi watsi da matakin soja kan mashigar Hormuz
Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Dokokin ƙasar kan rikicin Iran.

Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Dokokin ƙasar kan rikicin Iran, inda ya ƙi goyon bayan matakin soja da Amurka ke son ɗauka kan mashigar Hormuz.

Starmer ya jaddada cewa hanya mafi dacewa ita ce ta diflomasiyya, tare da nuna goyon baya ga tattaunawar da ake ci gaba da yi domin warware rikicin.

Ya kuma bayyana shirin jagorantar taron shugabannin ƙasashe tare da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a ƙarshen wannan mako domin tattauna halin da ake ciki.

Taron zai mayar da hankali kan neman mafita ta zaman lafiya da diflomasiyya, tare da duba yiwuwar ɗaukar wasu matakai na tsaro da za su tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci idan yanayi ya daidaita a yankin.

Starmer ya ƙara da cewa burinsu shi ne samar da tsari mai zaman kansa, na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe da dama, domin magance matsalar cikin tsari mai dorewa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use