Shugaban Amurka Donald Trump ya ce China ta amince cewa ba za ta tura makamai ga Iran ba, bayan wata wasika da ya ce ya aike wa shugaban ƙasar Xi Jinping.
A wani sako da ya wallafa a shafin sa na Truth Social, Trump ya kuma ce China na nuna gamsuwa kan batun bude mashigar Hormuz, yana mai cewa matakin zai taimaka wa kasuwancin duniya da kuma rage tashin hankali a yankin.