Limamin masallacin Usman bn Affan a Gwale, Jihar Kano, Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya, ya ce yawaitar cin amana da yaudara na daga cikin abubuwan da ke hana ‘yan Najeriya jin daɗin rayuwa da samun ci gaba.
Ya bayyana hakan ne a hudubar Juma’a, inda ya ce waɗannan halaye sun zama ruwan dare, suna haifar da matsaloli a rayuwar yau da kullum, ciki har da tauye ma’auni da ƙarya domin neman abin duniya.
Malamin ya kuma zargi wasu shugabanni da rashin kishin al’umma, tare da gargadin cewa neman mulki da kuɗi ta kowace hanya har da caca na ƙara lalata zamantakewa.
Ya buƙaci jama’a da su rungumi gaskiya da riƙon amana domin gyaran al’umma.