Hukumomin Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyu da ake zargi da aikata leƙen asiri da alaƙa da hukumar leƙen asirin Isra’ila, Mossad.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa an aiwatar da hukuncin ne da safiyar yau, bayan an same su da laifin shiga cikin wata cibiyar sadarwa ta leƙen asiri da ke aiki a ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun rika aikawa da bidiyon ayyukansu ga masu kula da su, tare da karɓar kuɗi ta hanyar fasahar kuɗin zamani (crypto).
Haka kuma, an ce an dade ana sa ido kan cibiyar kafin a gano cewa an ba ta sabuwar manufa ta kai hari kan wasu muhimman cibiyoyin gwamnati da na soji a birnin Tehran.
Binciken hukumomi ya nuna cewa an horar da su kan yadda ake kera abubuwan fashewa, zaɓar wuraren kai hari, da kuma ɗaukar hotunan wuraren da za a kai farmaki domin cimma nasara.