Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Najeriya ta maida martani ga Amurka, ta jaddada cewa ƙasar na cikin aminci

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga Amurka, inda ta jaddada cewa ƙasar na cikin yanayi na aminci, duk da gargadin da Amurka ta fitar kwanan nan na rashin tsaro. Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga Amurka, inda ta jaddada cewa ƙasar na cikin yanayi na aminci, duk da gargadin da Amurka ta fitar kwanan nan na rashin tsaro.
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga Amurka, inda ta jaddada cewa ƙasar na cikin yanayi na aminci, duk da gargadin da Amurka ta fitar kwanan nan na rashin tsaro.

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga Amurka, inda ta jaddada cewa ƙasar na cikin yanayi na aminci, duk da gargadin da Amurka ta fitar kwanan nan na rashin tsaro.

Ministan sadarwa na ƙasar, Mohammed Idris, ya bayyana cewa duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu yankuna, ba za a iya cewa harkokin tsaro sun taɓarɓare gaba ɗaya ba.

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta umarci wasu daga cikin ma’aikatan diflomasiyyarta da ayyukansu ba su da matuƙar muhimmanci da su fice daga babban birnin ƙasar, Abuja, tare da gargaɗin ’yan ƙasarta da ke shirin zuwa Najeriya da su sake tunani, sakamakon matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci da garkuwa da mutane.

Sai dai Ministan ya bayyana matakin na Amurka a matsayin shawara kawai, ba cikakken hujja na halin da ƙasar ke ciki ba.

Haka kuma, ya jaddada cewa matakan da gwamnati ke ɗauka a sassa daban-daban na ƙasar na ci gaba da rage matsalolin tsaro, tare da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use