Makarantar horar da sojoji ta NDA ta yi gargadi ga jama’a kan wasu ‘yan damfara da ke amfani da sunan kwamandanta wajen aikata zamba ta yanar gizo.
Hukumar ta bayyana cewa ana ƙirƙirar asusun bogi a kafafen sada zumunta domin yaudarar mutane da tayin ƙarya kamar kwangiloli da sauran damammaki.
Ta jaddada cewa ba ta da alaƙa da irin waɗannan saƙonni, tare da buƙatar jama’a su rika tantance sahihancin bayanai kafin su amince da su.
NDA ta kuma gargaɗi cewa duk wanda aka kama da hannu a irin wannan damfara zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa doka.
A ƙarshe, ta buƙaci jama’a su yi hattara tare da kai rahoton duk wani abu mai kama da zamba ga hukumomin da suka dace.