Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
CBN ya ƙara kuɗin katin ATM zuwa N1,500
Norway na shirin haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ƴan ƙasa da shekaru 16
Meta na shirin sallamar ma’aikata 8,000

Norway na shirin haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ƴan ƙasa da shekaru 16

Norway na shirin haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ƴan ƙasa da shekaru 16 Norway na shirin haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ƴan ƙasa da shekaru 16
Norway na shirin haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ƴan ƙasa da shekaru 16

Gwamnatin ƙasar Norway na shirin gabatar da wani sabon kudirin doka da zai hana yara ‘yan ƙasa da shekaru 16 amfani da kafafen sada zumunta, a wani yunƙuri na kare lafiyar su da tsaron rayuwarsu a yanar gizo.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, gwamnati ta bayyana cewa kudirin dokar zai ɗora alhakin tantance shekarun masu amfani da kafafen sada zumunta a kan manyan kamfanonin fasaha, domin tabbatar da cewa yara ba sa shiga shafukan da ba su dace da shekarunsu ba.

Matakin na Norway ya zo ne a daidai lokacin da ƙasashe da dama a Turai ke ƙoƙarin ƙara tsaurara dokoki kan amfani da kafafen sada zumunta, ciki har da Faransa da Spain.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use