Kamfanin Meta mamallakan Facebook da Instagram da Whatsapp ya ce zai rufe dubban guraben ayyuka a wata mai zuwa don mayar da hanakali wajen ci gaba da aiki da Kirkirarriyar Basira ta AI.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ga ma’aikatan ranar Alhamis, ya ce yana shirin rage kashi 10 na ma’aikata wanda ya kai kusan ma’aikata 8,000, tare da tabbatar da cewa ba zai maye gurbin su da wasu ba.
Sanarwar ta kara da cewa ‘babban dalilin da ya sa aka kori ma’aikata shi ne karin kudaden da Meta ke kashewa a wasu sassan kamfanin, ciki har da AI, wanda a bana zai kashe dala biliyan 135. Wannan ya yi kusan daidai da adadin da ya kashe a kan AI a cikin shekaru uku da suka gabata.
Mai magana da yawun Meta ya tabbatar da shirin yanke ayyukan amma ya ki yin karin bayani.
Mark Zuckerberg, wanda ya kafa Meta kuma shugaban zartarwa, ya yi tsokaci ga jama’a a watan Janairu cewa da gaske kamfanin zai sake rage ma’aikata a wannan shekara.
Shugaban Meta ya ce ya ga yadda ma’aikatan da suka dogara sosai kan kayan aikin AI suka zama, yana mai cewa mutum daya zai iya kammala ayyukan da a baya zai bukaci mutum biyu ko sama da haka.