Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya koka kan yadda Gwamnatin Najeriya ke ci gaba da dogaro da rancen kudi duk da cire tallafin man fetur, tare da gargadin cewa rashin tsarin kasafin kudi na iya lalata nasarorin da aka samu a baya-bayan nan.
Sunusi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na News Central a ranar Juma’a, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN ya ce yayin da cire tallafin man fetur da kuma sassauta farashin naira ya zama dole, lokaci ya yi da ya kamata a samu rangwame kan farashin kayayyaki da dama.
Sarkin Kanon ya ce “A koyaushe ina cewa tsarin tallafin mai ba zai dore ba, ba za mu iya ci gaba da tallafa wa matatun mai na kasashen waje ba, Najeriya kasa ce mai samar da mai, a bude matatun mai don su yi aiki’.
Ya kara da cewa, “A yau, muna da matatun mai na cikin gida, ba ma shigo da albarkatun man fetur ba, har ma muna fitar da kayayyaki zuwa Turai, kuma wannan yana da kyau ga tattalin arziki,” in ji shi.
Duk da goyon bayan sauye-sauyen, Sanusi II ya nuna damuwarsa kan yadda ake bi da bi, yana mai cewa aiwatar da manufofin ba tare da tsauraran kudade ba ya taimaka wajen faduwar darajar Naira.