Dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’adda uku a wani samame da suka kai a yankin Babbangida da ke Jihar Yobe, tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai na Civilian Joint Task Force.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Nanewa lokacin da dakarun ke sintiri suka ci karo da kwanton bauna da ‘yan ta’addan suka shirya musu.
Sai dai dakarun sun yi nasarar fatattakar maharan bayan fafatawa mai zafi, inda suka kashe uku daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.
Bayan artabun, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da kuma babura guda biyar da maharan suka bari a wurin.
An kuma bayyana cewa babu wani soja da ya jikkata a aikin, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri domin tabbatar da tsaro duk da cewa yankin na cikin yanayi na natsuwa amma har yanzu akwai fargaba.