Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Magoya bayan ADC a Jigawa sun yi zanga-zanga kan rikicin shugabanci

Magoya bayan ADC a Jigawa sun yi zanga-zanga kan rikicin shugabanci Magoya bayan ADC a Jigawa sun yi zanga-zanga kan rikicin shugabanci
Magoya bayan ADC a Jigawa sun yi zanga-zanga kan rikicin shugabanci

Magoya bayan jam’iyyar ADC sun gudanar da zanga-zanga cikin lumana a jihar Jigawa, inda suka nemi a amince da shugabancin jam’iyyar na ƙasa karkashin jagorancin David Mark.

Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun taru ne a ofishin INEC da ke Dutse, suna nuna rashin amincewa da yadda hukumar ke tafiyar da rikicin cikin gida na jam’iyyar.

Jagororin masu zanga-zangar sun bayyana cewa shugabancin da David Mark ke jagoranta shi ne sahihin shugabanci bisa tsarin kundin jam’iyya, tare da zargin INEC da nuna son kai a lamarin.

Sun kuma mika koke ga hukumar zabe, suna bukatar a dawo da shugabancin da suke goyon baya a shafin rajistar jam’iyyun siyasa, tare da gargadin cewa abin na iya barazana ga dimokuraɗiyya idan ba a gyara ba.

A nasa bangaren, jami’in INEC a jihar ya karɓi koken tare da tabbatar da cewa za a tura shi zuwa hedikwatar ƙasa domin duba lamarin, yayin da ake ci gaba da samun takaddama kan shugabancin jam’iyyar a fadin ƙasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use