Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan bindiga 100 a yankin Arbinda

Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan bindiga 100 a yankin Arbinda Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan bindiga 100 a yankin Arbinda
Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan bindiga 100 a yankin Arbinda

Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin Burkina Faso sun kashe kimanin ‘yan ta’adda 100 a wani samame da suka kai kusa da garin Arbinda.

A cewar bayanan da aka samu, an gudanar da wannan farmaki ne ta hanyar haɗin gwiwar hare-haren sama da kuma na ƙasa, inda aka fara da kai farmakin jiragen yaƙi kan sansanonin ‘yan bindiga da ke kusan kilomita 20 da arewa maso gabashin Arbinda.

Bayan haka, sojojin ƙasa suka ci gaba da kutsa kai cikin yankin domin kakkabe ragowar ‘yan ta’addan, a wani mataki da aka ce ya kasance cikin tsari da haɗin kai.

Majiyoyin tsaro sun ƙara da cewa harin ya jawo asara mai yawa ga ‘yan ta’addan, inda aka kashe kusan mayaka 100 a matakin farko na wannan samame.

Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci da kuma ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankin Sahel.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use