Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojojin sun yi ikirarin kashe mayaƙan Hezbollah 1,400

Sojojin sun yi ikirarin kashe mayaƙan Hezbollah 1,400 Sojojin sun yi ikirarin kashe mayaƙan Hezbollah 1,400
Sojojin sun yi ikirarin kashe mayaƙan Hezbollah 1,400

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun kashe akalla mayaƙan ƙungiyar Hezbollah 1,400 tare da lalata wurare sama da 4,300 da suka danganta da ƙungiyar, tun bayan ƙara tsananta hare-harensu a ƙasar Lebanon daga farkon watan da ya gabata.

A cikin wani sabon rahoto da suka fitar, sojojin sun ce rundunoninsu guda biyar na gudanar da hare-hare na musamman a lokaci guda a kudancin Lebanon, a matsayin wani ɓangare na faɗaɗa farmakin da suke kaiwa kan Hezbollah.

Sai dai a nata ɓangaren, Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce akalla mutane 1,888 ne suka rasa rayukansu tun bayan da hare-haren Isra’ila suka ƙaru daga ranar 2 ga watan Maris, ciki har da yara 163.

Wannan bambancin alkaluma tsakanin ɓangarorin biyu na ci gaba da nuna yadda rikicin ke ƙara tsananta, tare da jefa fararen hula cikin mawuyacin hali a yankunan da abin ya fi kamari.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use