Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 44 a hare-haren ‘yan bindiga a Kebbi

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 44 a hare-haren 'yan bindiga a Kebbi 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 44 a hare-haren 'yan bindiga a Kebbi
'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 44 a hare-haren 'yan bindiga a Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da cewa akalla mutum 44 ne suka rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyuka na jihar.

Sanarwar ta fito ne ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Bashir Usman, wanda ya bayyana cewa hare-haren sun auku ne a kauyukan Gebe, Kalkami, Kawara, Kasoshi, Awaye, Tungar Rini, Binuwa da kuma Debe.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tuni ta dauki matakai masu tsauri domin ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa, ciki har da gonaki, dazuka, iyakoki da kuma cikin al’ummomi, domin dakile sake aukuwar irin wannan lamari.

Hakazalika, ta tabbatar da cewa an dawo da harkokin yau da kullum da zirga-zirgar jama’a a yankin, yayin da aka jibge jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use