Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zargi tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam, da yunkurin kwace masa mulki tare da karɓar kujerarsa. Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi wasu mawaka a gidan gwamnati ranar Alhamis.
Gwamnan ya ce har yanzu bai ga takardar murabus ɗin tsohon mataimakin ba, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba ta yi masa wani laifi da zai sa ya ɗauki irin wannan mataki ba.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda aka tafiyar da al’amura a cikin tafiyar Kwankwasiyya, inda ya ce ba a tuntubi ‘ya’yanta kafin ɗaukar wasu manyan matakai a jam’iyya ba, lamarin da ke nuna rashin adalci.
Gwamna Yusuf ya mayar da martani ga masu sukar sa, yana mai cewa abubuwan da ke faruwa sun fallasa waɗanda ya kira masu cin amana da maƙiya a cikin tafiyar siyasa. Ya ce matakin da ya ɗauka ya fito ne domin kare makomar al’ummar Kano.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiki yadda ya kamata, tare da bayyana cewa akwai mutane masu nagarta da ke nuna sha’awar maye gurbin mataimakin gwamna.