’Yan bindiga sun kai hari garin Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama a Jihar Kwara, inda suka kashe masu gadin jeji biyar a wani sabon harin da ya sake tayar da hankalin al’umma.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da safiyar Juma’a, misalin ƙarfe 3, lokacin da maharan suka kutsa cikin garin kan babura, suna harbe-harbe ba kakkautawa. Lamarin ya jefa tsoro da firgici a zukatan mazauna yankin.
Wasu shaidu sun bayyana cewa maharan sun zo dauke da makamai masu nauyi, inda suka kai hari kan masu gadin jeji, ciki har da wasu sabbin jami’an da aka dauka aiki kwanan nan.
Sun kuma lalata tare da ƙone wasu ababen hawa na jami’an.
Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Jihar Kwara ko jami’an tsaro dangane da harin, yayin da mazauna yankin ke ci gaba da fargaba kan yiwuwar sake aukuwar makamancin hakan.