Rahoton hukumar agajin gaggawa ta Iran ya ce hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa kasar sun haifar da mummunar barna, inda aka lalata fiye da wuraren fararen hula 125,000.
Rahoton ya bayyana cewa barnar ta shafi gidaje, makarantu, kasuwanni da cibiyoyin kiwon lafiya, tare da ci gaba da ƙara ta’azzara halin da ake ciki.
Hukumar ta ce hare-haren sun fi shafar fararen hula, inda asarar ke ci gaba da karuwa a sassa daban-daban na kasar.