Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Nafiu Bala ya hana masu shekaru sama da 55 tsayawa takara a ADC

Nafiu Bala ya hana masu shekaru sama da 55 tsayawa takara a ADC Nafiu Bala ya hana masu shekaru sama da 55 tsayawa takara a ADC
Nafiu Bala ya hana masu shekaru sama da 55 tsayawa takara a ADC

Jam’iyyar ADC bangaren da Nafiu Bala Gombe ke jagoranta, ya sanar da cewa baza su bari masu shekaru sama da 55 su tsaya takara a karkashinsa inuwar ADC ba.

Nafiu ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya ce matakin na daga cikin shirin bai wa matasa cikakkiyar dama a siyasa.

Ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su jagoranci al’amuran siyasa, yana mai cewa sabbin tunani da kuzari daga gare su ne za su taimaka wajen gina kyakkyawar makomar kasa.

A cewarsa, tsoffin hanyoyin siyasa ba su bayar da sakamakon da ake bukata ba, don haka akwai bukatar bude kofar shiga siyasa ga matasa a matsayin ’yan takara da shugabanni.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use