Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Hare-haren ’yan bindiga sun tilasta hijirar mazauna kauyuka 21 a Sokoto

Akalla mazauna kauyuka 21 a jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu sakamakon barazanar hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa, kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Gidan Kare, Kaware, Chabi, Dattabi, Janwake, Sha Rana, Darbekami, Gidan Sule, Kuruwa, Mahuta, Dantayawa, Kawala, Bagirbe, Tsattsagi, Katsira, Imasa, Bela, Hura Girke, Galadimmai da Asha Ruwa.

Rahoton ya kara da cewa yawancin mutanen da suka tsere sun samu mafaka ne a garin Tureta da kewaye, inda suke fuskantar matsanancin yunwa da karancin abinci.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa da dama daga cikin wadanda suka tsere suna zaune ne a gidajen ’yan uwansu, maimakon a sansanonin ’yan gudun hijira.

Hakazalika, an ruwaito cewa sama da mutane 1,000 na kwana a makarantar firamare ta Abdulbaki da ke Tureta cikin cunkoso, ba tare da samun isasshen taimakon jin kai ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use