Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba za ta bari ’yan ta’adda su samu mafaka ba a ko’ina cikin ƙasar nan.
Ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar jaje da ya kai Maiduguri, Jihar Borno, bayan wani sabon harin da ya yi sanadin mutuwar manyan jami’an soja, ciki har da Birgediya Janar Oseni Braimah tare da wasu sojoji.
Shettima ya ce gwamnati na matuƙar jin tausayin iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, musamman sojojin da suka sadaukar da kansu wajen kare ƙasa.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da bai wa rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin fatattakar duk masu aikata laifuka.