Shugaban hukumar binciken gawarwaki ta Iran, Abbas Masjedi Arani, ya bayyana cewa an gano tare da tantance gawarwakin mutane 3,375 da suka rasa rayukansu a lokacin yaƙin Iran da Amurka-Isra’ila.
A cewarsa, daga cikin waɗanda suka mutu akwai maza 2,875 da kuma mata kusan 500, yayin da ake ci gaba da aikin gano sauran waɗanda har yanzu ba a kammala tantance su ba.
Rahoton ya ce an tattara waɗannan bayanai ne bayan hare-haren da suka yi sanadiyyar mummunar barna a sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu asarar rayuka.
Hukumomin Iran sun bayyana cewa an yi amfani da ƙwararrun likitocin binciken gawarwaki domin tabbatar da gano wadanda abin ya shafa.
Hukumar ta ana ci gaba da bincike da tattara ƙarin bayanai, kuma adadin na iya ƙaruwa ko kuma a fayyace shi da kyau yayin da ake kammala aikin tantancewar.